Daga Zulaihat M. Saeed
Shugabar Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK), Farfesa Sa’adatu Hassan Liman, ta bayyana cewa, yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da aka rattaba wa hannu kwanan nan tsakanin Jami’ar da Asibitin FMC da ke Keffi, an yi ta ne kawai domin haɗin gwiwa ta ɓangaren karatu da samun horon aiki na asibiti, ba wai miƙa mallaka ko tafiyar da gudanarwar asibitin ba.
Yayin da take jawabi a lokacin tattaunawa da manema labarai, Farfesa Sa’adatu ta ce, wannan ƙawance zai bai wa ɗaliban likitanci da na sauran fannonin kiwon lafiya na NSUK damar amfani da kayan aikin asibiti na FMC Keffi, ɗakin gwaje-gwaje, na’urori na musamman, da damar samun horo na aikace-aikace, yayin da kowace cibiya za ta ci gaba da riƙe ‘yancin kanta da nauyin da doka ta ɗora mata.
ƘARIN LABARI:
Tinubu Ya Bai Wa EFCC Umarnin Sakar Wa Asusun Jihar Osun Mara
Ta jaddada cewa, yarjejeniyar na da manufar ƙarfafa ilimin likitanci, binciken kimiya na magunguna da inganta fannin kiwon lafiya, inda ta buƙaci jama’a da su yi watsi da rahotannin da ke cewa Jami’ar ta karɓe ikon gudanar na FMC Keffi.
Kazalika, ta jaddada aniyar jami’ar na gina kyakkyawar haɗaka ta dabarun aiki da za su haɓaka ingancin ilimi tare da samar da ƙwararrun ma’aikatan kiwon lafiya.
