Daga Ishaq S. Hamza
Dakarun sojin Najeriya sun ceto wata mata mai shekaru 25, Rukaya Mohammed, tare da ‘ya’yanta biyu, bayan da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da ita a shekarar 2017 a Jihar Borno.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa, an ceto Rukaya da ‘ya’yanta, Hauwa Mustapha mai shekaru shida da Fati Mustapha mai shekaru huɗu, a yayin wani samame da sojoji suka kai a kusa da gadar Amuda a ranar 14 ga Agusta, 2026.
ƘARIN LABARI:
NSCDC Ta Damƙe Ɓarayin Babura A Nasarawa
Rahotanni sun ce Rukaya ta shaida wa sojojin cewa tun a 2017 aka sace ta sannan aka tilasta mata yin aure da wani ɗan ta’adda, inda ta zauna a Wunje.
Ta samu damar tserewa ne bayan wasu daga cikin ‘yan ta’addan suka bar sansanin sakamakon rikicin da ya ɓarke a tsakaninsu.
Dakarun sun mika Rukaya da ‘ya’yanta ga hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakan da suka dace.
